Posts

Showing posts from May, 2017

YAR BARIKI babi na daya

                'YAR BARIKI      ©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)       (01)     Kayataccen hotel ne na shak'atawa. Mafi akasarin mutanen dake zaune a farfajiyar wajen matasa ne da yawansu kuma 'ya'yan masu hannu da shuni ne. Mutane ne daga kabilu iri iri,ya had'a da larabawa da turawa uwa uba hausawa da fulanawa. Kowanne sha'anin gabansa kawai yakeyi ba ruwan wani da wani.       Lokacin k'arfe bakwai na daren alhamis. Daidai lokacin ne wata matashiyar budurwa sanye da siket wanda ko cinyoyinta bai gama rufewa ba da wata shegiyar riga wanda dashi da babu duk d'aya domin rabin jikinta daga saman wuyanta da kuma cikinta duk a bayyane suke. Kanta yasha gashin doki,ta tufkeshi da manya manyan ribbons har uku,maimakon tufkar ya kasance a tsakiya sai ya zamana a gefen b'arin kanta na dama. Fuskarta sai shek'i takeyi gata sarauniyar kyau. Lebban sun sha jan baki. (Nayi kyam rik'e   da alk'alamina ina duban irin takalmi mai t