Posts

Showing posts from November, 2017

SIRRIN HAJARA

DAYA R okon da nake a wurin Allah, nan a duniya har   can a lahira Allah sa muga annabi Muhammadu! Wadannan wasu jerin gwanon baituka ne daga cikin wata wakar shahararren shudadden mawakin nan mamman shata, suke tashi a hankali a gaban motar da muke ciki. A radiyon motar da watakila ya shafe shekara talatin yana shan duniya! Koda yake ba zan sa watakila ba saboda idan kiyasi zanyi da iya tunanina zan iya rantsewa ya kai shekara tamanin saboda yanzu na tabbata ma babu irin wannan samfurin akwatin radiyon a duniya. Ba radiyon bace kadai tsohuwa hatta motar da muke ciki da take tafe kamar zata hantsila idan muka hau gangara da tudu ta shafe sama da shekaru a duniya. Ni ba wannan ne ya dame ni ba, abunda ya dame ni kawai shine kallace kallace na dan ina taso in kalli yadda na tafi na dawo na tarar da kauyen namu.          Yana nan bai can za ba, duk da cikin dare ne amma farin wata ya haskaka komai. tun daga kan hanya nake gane hakan, saboda ban ga wani sau