SIRRIN HAJARA
DAYA
R
|
okon da nake a wurin Allah, nan a duniya
har can a lahira Allah sa muga annabi
Muhammadu!
Wadannan wasu jerin gwanon baituka ne daga cikin
wata wakar shahararren shudadden mawakin nan mamman shata, suke tashi a hankali
a gaban motar da muke ciki. A radiyon motar da watakila ya shafe shekara
talatin yana shan duniya! Koda yake ba zan sa watakila ba saboda idan kiyasi
zanyi da iya tunanina zan iya rantsewa ya kai shekara tamanin saboda yanzu na
tabbata ma babu irin wannan samfurin akwatin radiyon a duniya. Ba radiyon bace
kadai tsohuwa hatta motar da muke ciki da take tafe kamar zata hantsila idan
muka hau gangara da tudu ta shafe sama da shekaru a duniya. Ni ba wannan ne ya
dame ni ba, abunda ya dame ni kawai shine kallace kallace na dan ina taso in
kalli yadda na tafi na dawo na tarar da kauyen namu.
Yana nan bai can za ba, duk da cikin
dare ne amma farin wata ya haskaka komai. tun daga kan hanya nake gane hakan,
saboda ban ga wani sauyi da ya yi yawan da zai sa in fahimci wani abu ya sauya
daga tsarin kauyen ba, musamman ma da yake da rani na tafi na bar kauyen, yanzu
haka ma da rani na dawo dan haka shi yasa ban ga wani sauyi ba koda kuwa na
shuka ne
Motar ta tsaya a hankali a karkashin
wata darbejiya mai yawan ganyayyaki inda nan ne yake zama tashar ‘yan kauyen mu
idan sun hau mota daga inda muka hau wato kauyen magaji. Direban ya wage murya
da karfi yadda kowa zai ji ya fara sanarwa.
“Wadanda zasu sauka a kauyen TSAUNIN MARKE an kawo,
sai su yi hanzarin sauka dan muna sauri dare ne, muna so mu wuce”
Na kimkimi jakata ta baya irin ta ‘yan birni saboda
ko ba komai na je birni na yi shekara daya can dan haka ina da tabbacin na
waye, ba tare da jiran komai ba na nufi hanyar da zata sada ni da cikin kauyen
namu daga shararriyar hanyar da motar ta ajiye ni, saboda tun kafin mota ta
taso daga kauyen magaji ake amsar kudin kowa, na juya kadan dan naga ko akwai
wanda zai sauka sai na ga babu, harma motar ta fara tafiya a hankali cikin
kakarin ihun ta na tsufa da neman agajin hutawa
Ban damu ba na ci gaba da tafiya ta, na duba agogon
dake hannuna naga karfe daya da rabi da minti takwas na dare, na girgiza kai
ina gyara jakata dake wuya na, na tabbata sai na ba mutanen gida mamaki, yadda
nayo tafiyar dare haka da ban saba da ita ba
Ko kuma su, zasu bani mamaki
Na dan yi nisa kenan kafin na karasa cikin kauyen da
yake akwai ‘yar tafiya ta tazarar da ba zata wuce minti biyar ba. Haka kawai na
daga kai na kalli gefena na hagu kamar an dasa ni na tsaya ina kallon ikon
Allah, ina kallon wata doguwar mata mai dogayen kaya ta nufo hanyar da nake a
hankali, gabana ya so ya fadi saboda ba a kan hanya na ganta ba, ta cikin jeji
na ga tana tahowa, sanyin da kafafuna suka yi yasa na dan jinkirta kamar mai
jarumta, ta ratso ta cikin farin watan a cikin talatainin daren ta nufo ni,
ganin wurina tayo a hankali ya halittawa zuciyata tsoro mai yawa sosai, na kasa
motsawa ina jiran inji ar! In yanka da gudu, doguwa mai dogayen fararen kaya ta
nufo ni bata daina ba, kamar yadda zuciyata bata daina luguden tsorata ba, ta
karaso daf da ni a yananyin ta gaba daya babu tsoro sai dai akwai hawaye a tare
da ita, ta dan tsaya tana kallo na kamar yadda nake kallonta, sannan a hankali
na kai kallona kan kafarta da niyyar ko zanga kofato in yanka a guje, sai nayi
arba da wata siririyar kafa mai kyau da zubin yatsu masu tsayi masu kyawun
gani.
A lokacin na tabbata idan da za’a tsarga fatata bana
tsammanin za a samu jini na kai kawo, saboda yadda na ke cikin rudani.
Ta girgiza kai kawai ta juya ta kalli hanyar da na
fito da niyyar tafiya, ba tare da tayi min maganar ba kuma na ga ta juya din.
Gani ni kuma Allah yayi ni da matukar son jin kwakwaf! Da shegen son gulma,
hakan yasa na daga murya a hankali nayi mata magana
“Baiwar Allah
daga ina kike?”
Ta juyo a hankali kamar sitiyarin mota da fararen
dogayen kayan dake jikinta ta kalle ni kana ta sake juyawa har yanzu bata yi
min magana ba, da niyyar zata wuce, ni kuma na riga na kwadaitu da son jin daga
inda take ko yaya ne, tunda dai na tabbata ba aljana bace, dan da aljanace da
naga kofato! Dan haka sai na sake
tambayar ta karo na biyu
“Baiwar Allah daga ina kike, kuma ina zaki je?”
Ta sake juyowa tana kallona, gabana ya fadi ina
ganin kamar da zarar ta juyo zan ga ta juyo min da kan kura ko damisa ne! amma
da kanta ta juyo da kyakkyawar fuskar ta ta girgiza min kai, kana ta yi min
magana a hankali da siririyar muryar ta
“Daga duniya nake, kuma cikin duniya zani, ko akwai
inda ake zuwa bayan duniya?”
Na hadiye miyau dakyar kana na girgiza kai
“Babu, sai dai
bayan nan akwai lahira”
“To can zani”
“Lahirar?”
“Ko zaka hana
ne?”
Na yi sauri na girgiza kai tare da kauda kai yadda
naga ta zaro min idanu, kana na ji tayi wani dogon tsaki kana ta juya tana surutu
“mutane sai shegiyar tambaya kamar a gaban alkali, to ka biyo ni kaga inda
zanje”
Na girgiza kai tare da sauke numfashi ina tunanin
ina ni ina bin wannan doguwa mai dogayen kaya haka, bayan naji inda kika
ambata? Koda bata ambaci lahira ba ba binta zanyi ba, gida na nufa, ina
kallonta ta cikin farin watan tana ta tafiyar ta har tayi nisa ta haye titi ta
nausa cikin daji inda na tabbata akwai matsala koda da ranane balle da cikin
wannan uban dare, na juya na ci gaba da tafiya ta ina tunanin watakila lahirar
zata je da gaske, watakila neman mutuwa take saboda wani bakin ciki da aka sata
tunda ga hawaye nan a fuskar ta.
Na tabbatar shi kenan ni da ita mun rabu ba zamu
sake haduwa ba dan haka bari in cire tunanin ta a raina.
watakila yanzu
na fara ganinta
Haka na mike ina ta tafiya ta har na
shigo cikin kauyen, ina shiga na tarar da shagon na’ago a bude kamar yadda na
tabbatar a bude zan ganshi, saboda sama da shekara goma shagon shi a bude yake
kwana, da yake a jikin dakin sa yake kuma shi gashi gwauro wanda bai taba
dandana aure ba, tun zamanin iyayen mu suna ‘yan yara har ya zuwa yanzu haka
na’ago yake rayuwa shi kadai abunsa, na yi masa sallama. Na’agoya dago ya kalle
ni kana ya dauke kai abinsa ya sake ci gaba da murza shaken da yake murzawa na
gwangwani, ina tunanin shi har yanzu bai daina shaken nan ba, na zauna tare da
sauke numfashi ina washe baki da tsammanin ganin sa ya nuna mamakin gani na da
wannan dare, amma cike da mamaki yanayin sa gaba daya bai nuna haka ba, kamar
wanda muke tare tun dazu naje na zaga na dawo haka ya kalle ni, na daure na yi
masa magana
“Na’ago mai kwanan shago!
Ya baka nuna mamakin ganina cikin wannan talatainin daren bane?”
Na ago ya yi tsaki tare da shakar
shaken sa kamar babur din da ta saba da shake!
“Aikin banza wai giwa ta ga shaho na
shawagi” yaci gaba da shakensa tare da tari kamar mai ciwon taba! Yanda kasan
dole! Haka yake shan wannan shake yayi ta tari kuma kullum sai yayi kwalla
bayan ya gama shaken, “Yanzu fa baka fi minti talatin da barin nan ba, kuma sai
inyi mamaki bayan ba tafiya kayi ta shekara goma ba”
Nayi kasake ina kallon sa koda yake
nasan halin na’ago da ban dariya hakan yasa na fashe da dariya ina mamakin
yadda har yanzu bai bar shakiyancin sa ba, ya kalle ni kawai yana ganin kamar
na tabu.
“Ya kake yi min irin wannan ihun cikin
dare haka ko ko so kake ‘yan doka suzo su kama ni?”
“Ni ba ihu nake ba, dariya ce malam
na’ago, naji ne ka ce wai ban fi minti talatin da barin nan ba, shine na ke
dariya dan nasan ba haka bane”
“Hmm! ku dai yaran zamani da son kure
tsoffi! To ai koda na yi kari a kai ba zai wuce na minti goma ba, dan dai baka
fi minti goma sha biyar da barin shagon
nan ba, ko kana nufin ba kai bane kace zaka je dauko tarkon ka da ka sa na zomo?”
Na dan nutsu ina kallon malam na’ago
yadda yake ta zuba haka kamar indararo kamar kuma yanayin sa da gaske yake, na
sha mur dan yin magana da gaske
“Haba malam na’ago, me yasa kake irin
wannan maganar, ni yaushe na zo nan? Yanzu fa dawowa ta daga kaduna kenan,
birni inda na tafi shekarar data wuce da rani”
Ya dakata da jujjuya shaken sa da yake yi ya kalle
ni da kallon mamaki da hasala. Hawayen shaken da yake yi cike a idanunsa
“Ka tashi ka tafi ka bani wuri tunda
kai ma ka zama shashasha irin su mani mani, yaya zaka same ni dattijo kamata
kayi ta min wannan zubar? Ko an gaya maka hankali na ya fara kaucewa ne, dazu
fa ka wuce kayi yamma kana cewa zaka je ka dubo tarkon zomon ka. Yaya kuma zaka zo ka rika ce min
yanzu ka dawo kai aljani ne to?”
Tabbas da gaske yake, yadda naga ya
hakikice yana ta magana da tada jijiyar wuya na kalle shi sannan na kalli zoben
hajara dake hannuna wanda dazu da rana da zamu rabu a kaduna take kuka ta bani
tare da tabbatar min da in rike mata alkawarin soyayyarta. Amma gashi yanzu malam na’ago ya takarkare yana ta so ya maida ni wani
mutum biyu!
“Ni fa da gaske nake malam na’ago kuma
gaskiya bazan boye maka ba, kana so ka bani tsoro wallahi, yaushe ka ganni? Ni
da nayi tafiya shekara daya bana gida, yanzu da dawowata kace ka ga na wuce... .........?”
Zai daga min hannu tare da daka min
tsawa! Na san shi da masifa musamman idan yana da gaskiya, “Ko dai ka sha
tiramol yayi maka yawa ne jamilu?”
“Ai kaima kasan ina daya daga cikin
yaran da basa shan komai a kauyen nan na ‘ago”
“To ai shine nake tunanin ko ka fara
shane, kasan sabon shiga yafi buguwa, idan ba haka ba yaya zaka zo kace min ba
kai bane?”
“Ko dai shaken da kake sha yau mai
nauyi ne na’ago?”
Ni da kaina nasan bai kamata in fada
masa haka ba, saboda masifaffe ne ko ba haka bama, ya haife ni, ya zaro idanu
yana kallo na kana ya kwashe da dariya
“Ka ganni nan! Tun da nake babu wani
kayan maye da ya taba kauda min tunani na dai dai da dakika daya, nasha banju
na nasha wiwi, nasha taba, nasha sukudayi, nasha make uba, nasha garkami, nasha
kafso, kai in tabbatar maka a zamanin sarki sulaimanu mai madaci har giya nasha
a ranar bikin dakin sarautar sa, dan haka na fi gaban nan, nafi gaban kace
wannan dan karamin abun alhakin ya kauda min tunani na”
Na yi kasake ina kallon sa¸ lokaci daya
ya birkide kamar an aiko masa da sakon mutuwa, koda yake nasan baya son ana
karyata shi duk da akwai shi da shegiyar karya, na mike tare da daukar jakata,
dan na gaji da jin wannan tatsuniyar tashi ta almara, na kalle shi ina fita
daga cikin shagon nashi
“Kayi hakuri malam na’ago dama wasa
nake yi maka”
Ina jin shi daga can ciki yana min
magana cike da ihu da masifa
“Dama na san ni zaka rainawa wayau!
Lallai kaima ka shiga jerin wadanda zanci ubansu a kwanakin nan! kada kaga dan kana ANGO!!”
Kalaman sa na karshe su suka iso kunne
na da karfi, sune kuma suka sa na tabbatar da na’ago ya sha shaken da ya taba
kwakwalwar sa yau, da yake halin tsufa
“Kada kaga dan kana ango!”
Kalaman suka sake zuwa cikin kwakwalwata sune kuma suka
sani dariya har lokacin da na karaso kusa da kofar gidan babana inda naga taron
matasa sun kunna wuta da gungume icce suna gasa wasu kaji kamar yadda ake yi
idan anyi biki a kauyen, na yi murmushi amma har lokacin dariyar malam na’ago
bata barni ba, ina mamakin yadda tsoho kamar wannan yaki ya bar shake, lallai
kuwa kwanan nan shake yana gaf! Da shake kwakwalwar sa ya daina ganewa gaba
daya, ina karasowa daya daga cikin abokaina wato janaidu ya mike da sauri tare
da goge kwallar hayakin da ke fuskar sa ya kalle ni a dan hasale da fushi
“kai dan ka rainawa mutane hankali muna
gasa kajin nan amma sai ka wani kinkimi jaka ka tafi neman zomo, to yanzu so
kake kace mana ka kamo zomon?”
Cak! Numfashi na ya nemi daukewa, meke
faruwa ne? na fara nazari akan haka, kalaman janaidu naji suna so suyi kama da
kalaman malam na’ago
”
dazu fa ka wuce kayi yamma kana cewa zaka je ka dubo tarkon zomon ka. Yaya kuma
zaka zo ka rika ce min yanzu ka dawo kai aljani ne to?”
Na
tuno kalaman na’ago sannan yanzu ga abunda janaidu yake fada min
“kai dan ka rainawa mutane hankali muna
gasa kajin nan amma sai ka wani kinkimi jaka ka tafi neman zomo, to yanzu so
kake kace mana ka kamo zomon?”
Nayi shiru ina kallon sa. Ina mamaki,
mamaki sosai. Ba haka ya kamata su tare
ni ba, kamata yayi suyi ihu cikin murna amma sun tare ni da abunda zai juya min
hankali
“Muna maka magana dole kayi shiru tunda
baka da abunda zaka ce, bayan kasan ba haka ango ke kasance wa ba a duk lokacin
da akayi masa biki a garin nan” wadannan kuma kalaman dayan abokin nawa ne,
tanimu, na kalle shi shima mamaki bai barni na bashi amsar su ba, har sai da
alasan ya tabani tare da magana
“Ya kayi mana shiru muna yi maka
magana”
“Ai mamaki kuke bani ne, dan naji kuna
fadin wasu abubuwa da bansan da su ba” janaidu ya kalle ni yana rike da wukar
dake hannunsa wadda yake niyyar yankan naman dan dandanawa
“Haka kake dama ai jamilu, baka canzawa
kuma ba zaka canza ba duk da auren nan da akayi maka! Ya dai kamata kasan mutum
na sakewa a duk lokacin da akayi masa aure”
Na tsaya ina kallon su kamar wani gaula
saboda abun yana so ya bani dariya da kuma mamaki, janaidu ya sake yi min
magana wannan karon a fusace
“wai kai baka san mu bane ka zo ka
tsaya sai kallon mu kake yi? Ko ko a wurin kamun zomon ka yi gamo da wani abu
ne?”
Na
hadiye miyau sannan na kalle shi
“ka dauka cewa duk maganganun da kake
yi babu wanda nake ganewa a ciki, saboda ba kayi min su yadda zan gane ba
janaidu, yaya zaku tare ni da wadannan kalamai gatsau gatsau dasu ba kai ba
gindi? To idan ma wasa kuke yi zanso dan Allah ku janye dan ku barni da hutun
gajiyar da na sha”
Tanimu ya dan tsaya yana nazari na dan
ya fisu hankali shi yana da saurin fahimta¸nasan shi zai fada min gaskiya ba
zai yi min wasa ba
“hmm! me kake so to mu fada maka da ya
fi haka jamilu?”
Na kalli tanimu shi janaidu tuni haushi
yasa ya durkusa kasa ya bar mu yana gyaran naman kajin
“Tanimu nasan zaka fahimce ni, dan haka
kai ya kamata in fadawa gaskiya, yanzu fa na dawo daga tafiyar da nayi tun
waccan shekarar da ta wuce yaya zaku tare ni da wadannan kalaman na wauta da
basu dace ba, dan Allah ku fada min waye yayi aure a cikin ku?”
A yanzu gaba dayan su suka dago suna
kallo na, da wani irin kallo na mahaukaci, alasan dama mugun matsoraci ne, tuni
ya ja da baya yana kallo na daga baya baya, janaidu ya kauda maganar fushi daga
fuskar sa yana nazarina
“Idan so kake mu nanata maka abunda
kaima nasan ka sani shine, aurenka ake yi
jamilu! Auren ka ake yi kai da masoyiyar ka!”
Na dan yi kasake karo na barkatai ina
kallon su, tabbas a yanayin su da gaske suke. Aure na ake yi kamar yadda suka
fada
Amma yaushe nace musu ina so?
Na numfasa cikin bacin rai
“Dama har yanzu ba a daina auren kaka
da kakanni ba janaidu?”
Janaidu
ya gyada kai
“Ai ban san irin auren da kake magana
ba jamilu”
“Na dauka an daina aure ba tare da
mutum yana nan ba, na dauka an daina aure ba tare da sanin ma’auratan
ba..........”
Alasan ya numfasa a dan tsorace har
yanzu
“To ai kai da saninka, kai da
amincinka, tunda har ruwa sai da aka kai rana akan ka bari sai badi, amma kayi
tsalle ka bidire akan dole sai an yi maka”
Mamakina
yanzu yana so ya nunku
“Ban
gane ba!”
“Me
kake so ka gane?” inji janaidu
“Ni fa bani aka yi ma auren nan ba, wai
baku yarda yanzu dawowa ta kenan daga birni bane?”
Tanimu
ya bani amsa da tambaya.
“Wai baka yarda kai ne kayi auren nan
bane jamilu? Ko ka fara taurin kai ne?”
Janaidu
ya kalle shi
“Wannan ba taurin kai bane, rainin
wayau ne, dan haka mu fasa maganar cin kajin nan muje mu raka jamilu dakin
matar sa dan ya nuna mana alamun ya zaku da yawa ne”
Suka kalle ni da gaske suke, ganin zasu
maida ni mahaukaci yasa na daka musu tsawa cikin fushi da tada jijiyar wuya dan
nima fa masifaffe ne idan naga za’a raina min wayau
“Bana son iskanci da rashin hankali! Me
ya same ku ne? kun sha kwaya ne janaidu!! Yaya zaku zo ku tirke ni ku na min
maganganun da ban sa da su ba? Ni ban san wata amarya ba, hasalima ban san nayi
aure ba, gaba daya ma yanzunnan na dawo
daga birni tun tafiyar da nayi shekarar bara da ta wuce, yaya zaku maida ni
kamar na fita daga hayyaci na? haba ku natsu mana, ku fada min idan anyi min auren dole ne kuke jin nauyin fada min
wallahi hankali na zai fi kwanciya akan kuna so ku maida ni wani shashasha”
Yanzu sun tabbatar da gaske nake, sun
tabbatar da cewa watakila nayi gamo, na fahimci hakan ne ta hanyar wani kallo
da suke yi min kana suka kalli junansu, alasan ya kalli tanimu
“Shin wai tanimu! Da sanyi ne kadai
aljanu suka fi saurin kama mutum?”
Tanimu
bai gane me yake nufi ba
“Ban
gane ba, me yasa ka tambaya?”
Ya nuna ni da hannu yana rawa
“Da sai in ce tabbas jamilu gamo yayi
da aljanu!”
Janaidu ya kalli alasan a fusace
“Lallai kuwa da aljanin da ya kama ango
a daren auren sa na farko da ya cika tsinannen aljani mara tausayi! Amma kuma
ina ga kamar haka ne, kamar jamilu yayi gamo da mummunan aljanu masu birkida
tunani”
Raina ya baci sosai, na kalle su tare
da nuna su da yatsa
“Kada ku maida ni mahaukaci mana,
alhalin kune mahaukata, kuna maganganun da ban san kansu ba, a gidan ubanwa
aljani ya kamani?”
Tanimu
ya ce
“Ai gani suka yi ka rikice ne, tare da
kai fa muke tsaye a nan dazu, tare muka yanka kajin nan, kuma tare muka fige su, duk ma ba wannan
ba, kana nufin duk soyayyar da kuka yi da RUDA ba kai bane? Duk
soyayyar da kuka shafe tsawon shekara daya da wasu watanni ba kai bane? Haba
jamilu kuma sai mu yarda ba gamo kayi da aljanu ba?”
I zuwa yanzu kaina ya fara ciwo, me wadannan suke so su fada min? me ke
faruwa ne? yaushe na yi soyayya da wata mai suna RUDA? Yaushe na yi soyayya da ta
kai tsawon shekara daya a nan garin? Na tabbata dai na taba yi amma a birni,
amma a kaduna da naje nayi da masoyiya ta hajara ‘yar gidan da naje nake neman
kudi a can? Amma ya zasu ce min haka?
Na dukar da kai tare da dagowa na kalli
tanimu
“Ni dai na san ba ni bane, dan ni yanzu
na dawo daga birni, dan haka duk inda zamu je a duniya sai dai muje zan
tabbatar muku da kune kuka haukace, watakila kuma kune ma kuka yi gamo da
aljanu. Ni kunga tafiya ta wahalar gajiya bata sake ni ba”
Na juya kenan, janaidu ya kamo ni, na
juyo tare da sa hannu na hankade shi yayi taga taga zai fadi, matsoraci alasan
ya ja da baya da sauri yana shirin guduwa, tanimu ya dakatar da janaidu,
janaidu ya kalle shi a fusace
“Na rantse da kwarankwatsi! Nasha aradu
nasha yasin! Sai ya zo munje dakin amaryar sa, yaya kuke so ya maida ku wawaye
ne? kun manta da yadda angwaye a garin nan kunya ke sa su guduwa, ranar farko? Dan haka yanzu ma jamilu so yake ya
gudu da wayau washe gari a kira mu wawaye dan mun kasa kai ma amaryar sa shi”
Suka kalli juna, alamun yarda suka zo
musu, sannan suka fashe da dariya, alasan ya kalle ni
“Amma anyi shakiyi jamilu! Ai bamu san
haka bane gashi har ka tsorata mu wallai”
Ina ji ina gani suka cukume ni tun ina
tirjiyewa cike da hayaniya har suka kimkime ni suke yi cikin gida dani, sai da
aka nufi dakin da naga anyi ma feshi da farar kasa irrin ta amare naji gaba na
ya yanke yayi wata bahaguwar faduwa, sai lokacin tunanin wani abu yazo min a
raina
AKWAI CI GABA....
Comments
Post a Comment