YAR BARIKI babi na daya

                'YAR BARIKI
 
   ©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
  
   (01)

    Kayataccen hotel ne na shak'atawa. Mafi akasarin mutanen dake zaune a farfajiyar wajen matasa ne da yawansu kuma 'ya'yan masu hannu da shuni ne. Mutane ne daga kabilu iri iri,ya had'a da larabawa da turawa uwa uba hausawa da fulanawa. Kowanne sha'anin gabansa kawai yakeyi ba ruwan wani da wani.

      Lokacin k'arfe bakwai na daren alhamis. Daidai lokacin ne wata matashiyar budurwa sanye da siket wanda ko cinyoyinta bai gama rufewa ba da wata shegiyar riga wanda dashi da babu duk d'aya domin rabin jikinta daga saman wuyanta da kuma cikinta duk a bayyane suke. Kanta yasha gashin doki,ta tufkeshi da manya manyan ribbons har uku,maimakon tufkar ya kasance a tsakiya sai ya zamana a gefen b'arin kanta na dama. Fuskarta sai shek'i takeyi gata sarauniyar kyau. Lebban sun sha jan baki. (Nayi kyam rik'e  da alk'alamina ina duban irin takalmi mai tsinin dunduniya dake sanye a kafarta tare da mamakin yanda bata ko tsoron ya karya mata k'afa. Ganin zata b'acemin ya sanyani watsar da tunanina nabi bayanta a guje yayin dana bar Hanne cillare a bayana tana cillara k'afafuwanta wanda hakan ya tunomin da Kayan moh...(Hasken Idaniya..na tagwayen marubuta...lol).

    Cikin takunta mai sanya zuciyar dukkan wani d'a namijin da yayi kicib'us da ita motsawa take tafiya bata tsaya ko'ina ba sai gaban teburin wasu 'yan mata su uku wadanda duk cikinsu suma babu mai shigar arziki.

    "Sexy angel"

  Cewar wani bature dake zaune a kusa dasu, ya lumshe ido saboda wani irin k'amshi da ya busoshi.  Bata ko kalleshi ba saidai ta murmusa saboda ta karanci da ita yake. Tsinken sigari ta janyo ta sanya a bakinta kafin tayi amfani da lighter ta kunna.

     "Baby wallahi mutuminki yayi fushi,munkai (30mins) zaune tare dashi yana jira yaga b'ullowarki amma...."

   Wacce aka kira da sunan Baby,ta dakatar da ita ta hanyar watsa mata kallo da shanyayyun idanuwanta,kafin ta fesar da hayak'in sigarin. Cikin zazzak'ar muryarta tamkar sarewa marar tashi sosai

     "Ya kamata by now ace kin fahimceni sosai Manal, banason a dunga yimin karan tsaye a sha'anina ok? Da nasan ya bar nan da babu abunda zaisa nazo ."

  Tana gama fad'in haka ta mike da niyyar tafiya,baturen nan ya katse mata hanzari

    "Excuse me."

  Bata ko kalleshi ba tayi gaba tana karkada jiki. Manal ta dubi yan matan nan kafin taja tsaki

     "Zaman me mukeyi kuma? Saiku tashi mu wuce tunda 'yar mulkin tayi halin nata. Ta sanya muzo mu jirata,tayi mana rashin arzikin."

  'Yar bak'ar cikinsu ta bugi tebur daidai lokacin da baturen nan ya katsesu da tambayar lambar wacce suka kira Baby. Harararsa sukayi kafin su bar wajen. Akan hanya bak'ar ciki wato Dalal ta ja tsaki

     "Guy dinnan baisan wacece Baby ba da baiyi gigin tambayarmu lambarta ba."

   Manal ta tab'e baki

  "Kowane gayu idan ya tashi baby,baby. Sai kace muma ba mata bane. Ji fa yanda guys din wajen nan suka bita da kallo tamkar ita kad'ai ce mai abun kallo a jiki. Naga muma dai muna da dirin jikin nan da kyawun fuska ko? Me tafi sauran mata ne?"

   Hibba wacce tun soma maganarsu batace dasu uffan ba ta saki dariya a daidai lokacin da Manal ke kokarin bud'e mota. Wannan yasa duk suka kalleta da alamar tambaya na me kuma ya bata dariya haka?

   Hibba ta cigaba da magana

     "Kuna b'ata lokacinku wajen had'a kanku da Baby Tasleem. Wallahi tayi mana zarra,ku nifa tunda nake a rayuwata ban tab'a cin karo da gogaggiyar 'YAR BARIKI ba wacce komai nata daidai da fushinta ke burgeni ba kamar Tasleem. Ta cancanci a kirata baby domin wallahi ku kanku kun sani daidai da mayuka da turarukan da take amfani dasu abun kallo ne. Ai samun guy irin KB wanda zai tsaya maka akan komai wanda ko mijinka sai haka abu ne da mai matukar wuya. Abu na gaba da zai k'ara tabbatar maku ita d'in ta dabance,ba kowane shara take mu'amala dashi ba. Wallahi komai muk'ami da kud'in mutum idan har bai yiwa Tasleem ba toh koda yafi kare naci karan kanku ne kunsan ba kulashi zatayi ba. Wannan sai mu."

   Ta k'arashe tana 'yar dariya,inda ta k'ara k'ular da Manal da Dalal. A fusace Manal ke tuk'in har suka haura titi suka fita daga hotel d'in na Tahir. Kwarai su ukun sun kasance amininan baby saidai suna matukar kishin yanda ta fisu da komai,ta k'etaresu a harkar bariki. Haka Hibba tayi ta dariya tana k'ara b'ata ransu.

                    *******


  Baby Tasleem bata tsaya a ko'ina ba sai kofar gidan KB. Hon d'aya tayi,maigadin yayi azamar wangale mata k'ofa sanin ko wacece ita ga maigidan. Da gudu ta shiga harabar gidan ta faka motarta ta fito. Cike da yanga ta nufi cikin gidan kai tsaye.... ..!

Comments

Popular posts from this blog

SIRRIN HAJARA